Home / Art / Hausa al'adu / Buhari Yana Tare Da Wadanda Ba Su Son Ci Gaban Gwamnatinsa, Inji Rabran Mbaka
buhari mbaka

Buhari Yana Tare Da Wadanda Ba Su Son Ci Gaban Gwamnatinsa, Inji Rabran Mbaka

Daga Sani Musa Mairiga
Babban Limamin majami’ar Adoration ministry dake Enugu, Rabaran Ejike Mbaka ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana aiki tare da wasu wadanda ba su son gwanatinsa ta samu nasarar manufofi da kuma shirye-shiryen da ta sanya a gaba. Inda ya yi kira ga shugaba Buhari da ya gaggauta korar wadanda tsohuwar gwanatin PDP ta nada su a mukamai dabam-dabam,cdomin sune masu yi wa shugaban kasar makarkashiya da kuma kulla masa gadar zare.

 
Rabaran Ejike Mbaka ya bayyana hakan ne a lokacin da yake hira da ‘yan jaridu bayan kammala bikin yaye wasu matasan yakin Niger Delta wadanda suka samu hora a kamfanin kira robobi dake Enugu a karkashin shirin gwamnatin taraiya na samarwa matasa ayyukan yi.

 
Rabaran Mbaka yace idan har Buhari yana son samun nasara a gwamnatinsa to dole ne ya yi waje rod da sauran ‘yan PDP dake cikin gwamnatinsa. Inda ya bayar da misalin cewa abinda ke faruwa a gwamnatin Buhari a yanzu tamkar kamar mai kiwon kifi ne wanda bai san cewa akwai kadoji boye cikin kifayen ba, wadanda suke cin kifayen.
Mbaka ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kara hakuri su kuma ci gaba da yi wa shugaban kasar addu’ar samun nasara tare da shawo kan matsalolin da kasar nan ta samu kanta.

 
Ya ce duk wanda ke son gurgutan gwamnatin Buhari, to Allah zai tarwatsa shi, saboda shine mai bayar da mulki ga wanda yake so a kuma lokacin da ya ga dama kuma babu wanda ya isa ya ja da shi.

Send Money To Nigeria Free

About AbubakarMuhd

x

Check Also

TInubu osinbajo

APC Convention: Aspirants Trimmed To 2, Osinbajo And Tinubu – Senator Gaya

The number of aspirants has been trimmed to only Vice President Yemi Osinbajo and Bola Tinubu, says Senator Kabiru Gaya. #APCPresidentialPrimaries #APCSpecialConvention  The number of aspirants has been trimmed to only Vice President Yemi Osinbajo and Bola Tinubu, says Senator Kabiru Gaya.#APCPresidentialPrimaries#APCSpecialConvention pic.twitter.com/95BhZslGhf— Channels Television (@channelstv) June 7, 2022