Rikicin majalisar wakilai kan badakalar aringizon kasafin kudi na kara ta’azzara bayan da majalisar ta gayyato hukumar EFCC kan ta tuhumi tsohon shugaban kwamitin kudi na majalisar, Jibrin Abdulmumini wanda ya fallasa batun aringizon.
Majalisar dai na son EFCC ta fara binciken Hon. Jibrin ne tun daga lokacin da yake shugaban kwamitin kudi na majalisa a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2014 inda suke zargin ya fice wajen aringizon kasafin kudi ta yadda har sai da ya sanya tsohon Shugaban majalisar, Aminu Tambuwal kuka.
Wata majiya daga majalisar ta nuna cewa tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya hana Tambuwal daukar matakin ladaftarwa a kan Hon. Jibrin. Shugaban kwamitin majalisar kan Yada labarai, Hon. Abdulrazak Namdas ya tabbatar da cewa majalisar za ta ladaftar da Hon. Jibrin kan wannan zargi da ya gabatar a akan shugabannin majalisar.
Cc-Rariya