Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya fita daga jerin mutane 100 da suka fi arziki a duniya inda a halin yanzu ya kasance mutum 101 na attajiran duniya. A watan Maris da ta gabata, Dangote ne mutum na 51 a jerin attajiran amma sakamakon yanayin da tattalin arzikin Nijeriya ya samu kansa, darajar kadarorinsa ya ragu matuka Inda ya koma mutum na 71 kuma tun daga lokacin ya ci gaba da yin kasa.
Sai dai ana sa ran idan Attajiran ya kaddamar da kamfaninsa na sarrafa suga a shekarar 2019 wanda shi ne mafi girma a duniya, zai zama cikin mutane 20 da suka fi arziki a duniya.
Home / Art / Hausa al'adu / Yanayin Tattalin Arziki Ya Fitar Da Dangote Daga Jerin Attajiran Duniya 100
Tagged with: Hausa