Home / Art / Hausa al'adu / ‘Yan Fashin Sun Kashe ‘Yan Sanda Biyu Tare Da Raunata Guda Uku A Yayin Da Suka Kaiwa Wata Motar Banki Farmaki
money van

‘Yan Fashin Sun Kashe ‘Yan Sanda Biyu Tare Da Raunata Guda Uku A Yayin Da Suka Kaiwa Wata Motar Banki Farmaki

Wasu gaggan ‘yan fashi sun kashe jami’an ‘yan sanda guda biyu tare da raunata guda uku, a yayin da suka kaiwa wata mota mallakar babban bankin kasa farmaki a daidai tsaunin Hawan Kibo dake kusa da garin Riyom a jihar Filato.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Terna Tyopev ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai cewa ‘yan fashin sun kaiwa motar farmaki ne, inda uku daga cikin ‘yan sandan da suka rako motar suka samu rauni.

 
Motar dai tana dauke ne da kudi inda ta taho daga garin Jos za ta je garin Lafiya babban birnin jihar Nassarawa.
Saidai kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa barayin ba su yi sa’ar tafiya da kudin ba kasancewar jami’an sun yi gaggawar daukar mataki. Sannan kuma suna kan ci gaba da gudanar da bincike domin gano barayin.

 

Rariya

Send Money To Nigeria Free

About AbubakarMuhd

x

Check Also

found

Cigiyar Iyayen Yaron Da ‘yan Sandan Jihar Taraba Suka Kubutar Da Shi

Daga Shafin Biyora Adamu Aliyu Dan shekara Goma sha biyu daga unguwar Na’ibawa ‘Yan Lemo Kano jami’an ‘yan sanda a jihar Taraba sun sami nasarar kubutar da shi. Idan ‘yan uwansa sun gani ko wanda ya san shi sai ya tuntubi hukumar ‘yan sanda ta jihar Taraba. Gani nayi a Facebook na kwafo….. bani da masaniya akan lamarin… nayi ne kawai ko Allah zaisa ‘yan uwansa su gani a posting dina…..