Home / News From Nigeria / Breaking News / Sarkin Garin Ankpa Dake Jihar Kogi Ya Rasu
ya-rasu

Sarkin Garin Ankpa Dake Jihar Kogi Ya Rasu

Daga Aliyu Ahmad
A jiya Litinin ne Allah ya yi wa Sarkin garin Ankpa, Yakubu Ahmodu, rasuwa bayan ya yi shekaru 73 a duniya sakamakon gajeruwar rashin lafiya da ya yi. Wata majiya daga fadar masarautar ta bayyana mana cewa marigayi Sarkin, a ranar Lahadin da ta gabata ya halarci taro kan harkokin Musulunci da aka gudanar a garin Benin kafin ya bar duniya a washegari. Marigayin ya hau sarauta ne a ranar 7 ga Agusta, 1993. Ya rasu ya bar mata, yara da jikoki da dama.

Send Money To Nigeria Free

About AbubakarMuhd

x

Check Also

Labari Cikin Hotuna

Labari Cikin Hotuna

Shugaban Rundunar Sojojin Sama, AVM Sadik Abubakar Ya Jagoranci Dakarunsa Na Yankin Arewa Maso Gabas Wajen Gudanar Da Bikin Sallah.